logo

HAUSA

Sin ta musanta kalaman firaministan Birtaniya game da manufar Sin ta kandagarkin annoba

2022-06-29 21:55:48 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya musanta kalaman firaministan Birtaniya, game da manufar Sin ta kandagarkin annobar COVID-19.

Yayin taron manema labarai na Larabar nan, Zhao Lijian ya ce Birtaniya za ta ci gaba da tafka kura kurai, tare da jefa jama’ar ta cikin mawuyacin hali, idan har ta ci gaba da sanya batun “dimokardiyya ko mulkin danniya” cikin harkar yaki da annoba.

Yayin da yake amsa tambayoyi kan hakan, Zhao Lijian ya ce Sin na nacewa babbar manufar kandagarkin annobar COVID-19 a duk inda ta bulla, da dakile bazuwar ta cikin sauri, kuma bisa farashi mafi karanta. Kana tana matukar kare rayuka da lafiyar al’ummar kasar, tare da takaita mummunan tasirin annobar kan tattalin arziki, da ci gaban zamantakewar al’umma. Jami’in ya ce wannan mataki mai ma’ana, ya shafi dukkanin al’ummar duniya ne ba wai kasar Sin kadai ba.