logo

HAUSA

Sakon Xi ya karfafa gwiwar matasan Afrika wajen raya huldar Sin da Afrika

2022-06-16 11:18:45 CMG Hausa

Aikewa da sakon da Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya yi cikin lokaci, ga wasikar da mahalarta taron karawa juna sani na kungiyar ‘yantar da kudancin Afrika na shekarar 2022, ya yi matukar kara kaimi ga matasan Afrika.

Nawanda Yahya, jagoran mahalarta taron daga kasar Tanzania, ya bayyana cewa, samun sakon amsa daga shugaba Xi cikin kasa da mako guda, wani kwarin gwiwa ne ga bangarorin matasan Afrika, da shugabannin da suka halarci taron na makonni biyu, a makarantar nazarin mulki ta Mwalimu Julius Nyerere, dake gundumar Kibaha a gabar tekun kasar Tanzania.

Shugabannin makarantar tare da hadin gwiwar jam’iyyu shida na kudancin Afrika da suka hada da, jam’iyyar CCM ta Tanzania, da jam’iyyar ANC ta Afrika ta kudu, da jam’iyyar ‘yantar da Mozambique, da jam’iyyar ‘yantar da jama’ar Angola, da jam’iyyar SWAPO ta Namibia, da kuma jam’iyyar ZANU-PF ta Zimbabwe.

Marcelina Chijoriga, shugabar makarantar Mwalimu Julius Nyerere ta yi martani tare da nuna amincewa da samun sakon wasikar daga shugaba Xi, inda ta ce, wannan wani babban al’amari ne wanda ke kara haifar da kyakkyawan fata ga matasan jam’iyyu shida na Afrika, har ma da nahiyar Afrika baki daya. (Ahmad)