logo

HAUSA

Sabon Layin Dogo Da Ya Zagaye Hamada Mafi Girma A Kasar Sin Ya Fara Aiki

2022-06-16 21:09:28 CMG Hausa

Alhamis din nan ne, aka fara aiki da sashin karshe na layin dogo mai tsawon kilomita 2,712, wanda ya zagaye hamada mafi girma a kasar Sin, wato Taklamakan, dake yankin arewa maso yammacin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, bayan da aka shafe shekaru 3 da rabi ana kokarin ginawa.

Sabon sashin layin dogon mai nisan kilomita 825, ya tashi ne daga gabas da birnin Hotan zuwa gundumar Ruoqiang, kusa da gefen kudu da Taklamakan, hamada ta biyu mafi girma a duniya mai cike da yashi, inda kusan kashi 65 na layin dogo yake gudana cikin hamadar.

Bude layin dogo zai baiwa jiragen kasa damar zagaya da'irar hamadar dake zama karo na farko a duniya. Haka kuma, layin dogon zai saukaka jigilar kayayyaki da tsare-tsaren wasu sana'o'i dake yankin Xinjiang da suka hada da auduga, da dangin gyada, da dabino, da ma'adinai.

A yau, fasinjoji sun yi tattaki zuwa tashar layin dogo da ke birnin Hotan, domin yin balaguro a karon farko a cikin wani jirgin kasa da ke gudun kilomita 120 a cikin sa’a guda, wanda kuma zai taimaka wajen saukaka tafiye-tafiye da inganta rayuwarsu.

Don taimakawa wajen kare hanyar dogon, an gina gadoji guda biyar, inda mafi tsayi daga cikinsu, ya kai fiye da kilomita 18, don daga layin dogon zuwa wani tsayin shinge wanda zai kare shi daga illar guguwar yashi.

Bugu da kari, an samar da wani ziri maras gurbata muhalli, mai kusan murabba'in mita miliyan 50 na ciyayi, inda aka shuka bishiyoyi miliyan 13, wadanda ake fatan za su ba da kariya ga sassan da ake ganin yashin zai iya yi musu illa.(Ibrahim)