logo

HAUSA

Kasashen BRICS sun yi kira a hada kai don tinkarar sauyin yanayi

2022-05-15 17:28:35 CMG Hausa

Kwanan nan ne aka gudanar da babban taron kasashen BRICS kan tinkarar sauyin yanayi ta kafar bidiyo, inda aka yi kiran a hada kai don tinkarar matsalar sauyin yanayi, da tattaunawa kan gaggauta rage fitar da iskar dake gurbata muhalli, da lalubo hanyar samun farfadowa mai dorewa da daidaito da nuna hakuri.

Ministan kula da muhallin halittun kasar Sin, Huang Runqiu ya gabatar da jawabin dake cewa, ta hanyar shirya babban taron kasashen BRICS kan tinkarar sauyin yanayi, kasar Sin na fatan yin kokari tare da kasashen BRICS, don tabbatar da aiwatar da ra’ayin kasancewar bangrori daban-daban a duniya, gami da yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya da kuma yarjejeniyar Paris, a wani kokari na kafa tsarin kula da yanayin duniya mai adalci da samar da moriya ga kowa, da kiyaye duniyarmu yadda ya kamata. Minista Huang ya kuma bayyana manufofi gami da matakan da kasarsa take dauka a fannin sauyin yanayi.

A nasa bangaren, wakilin kasar Sin na musamman mai kula da harkokin tinkarar sauyin yanayi, Xie Zhenhua ya nuna cewa, kasarsa tana goyon-bayan kasar Masar wajen gudanar da taro karo na 27 na kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi ta MDD, wato COP27 a takaice, don yin kokari tare da bangarori daban-daban, wajen gudanar da taron cikin nasara. (Murtala Zhang)