logo

HAUSA

Xi ya jaddada inganta zamanantar da ayyukan gwamnati da ci gaba da yin gyare-gyare a kasafin kudi

2022-04-20 14:00:31 CMG HAUSA

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, jiya Talata ya jaddada bukatar kara kaimi, don zamanantar da aikin gwamnati, da ciyar da aikin gyare-gyaren tsarin kasafin kudi a matakin larduna da kasa da haka. Shugaba Xi ya bayyana haka ne, yayin da ya jagoranci taro na 25 na kwamitin tsakiya na zurfafa yin gyare-gyare daga dukkan fannoni. .

Xi ya kara jaddada bukatar kara azama, wajen bullo da wani tsari na kara karfin kasar Sin a fannin binciken sararin samaniya, inda ya bukaci a rika amfani da fasahar zamani, wajen tafiyar da hidimomi da ayyukan gwamnati.

Bugu da kari, Xi ya bayyana cewa, ya kamata a inganta harkokin fasahar zamani da na basira, don ba da cikakken goyon baya ga zamanantar da tsarin tafiyar da hidimomi da harkokin kasa.

Dangane da gyare-gyaren tsarin kasafin kudi na cikin gida kuwa, shugaba Xi ya bayyana cewa, ya kamata a daidaita huldar kudi tsakanin gwamnatoci a matakin larduna da kuma kasa da haka, don samar da daidaito mai ma'ana tsakanin iko da sauke nauyi, da samar da daidaiton rabon kudaden shiga, da daidaita albarkatun kasa, da tsarin hada-hadar kudi na cikin gida, da kasafin kudi mai inganci a matakin farko.

Shugaba Xi ya kuma yi kira da a gaggauta gina kasuwar cikin gida ta bai daya, da inganta daidaita ayyukan yau da kullum na jama'a da bunkasa samar da ci gaba mai inganci. (Ibrahim)