logo

HAUSA

Amurka tana kara cimma moriya daga tada yake-yake da sanya takunkumi

2022-04-06 20:54:58 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Laraba cewa, yake-yake da kakaba takunkumi, sun haifar da matsalar tururuwar ‘yan gudun-hijira, da ficewar kudade daga turai, gami da karancin makamashi a nahiyar Turai. Amma a hannu guda Amurka, tana kara cimma moriya, da samun kudade masu tarin yawa daga yake-yake da takunkumin.

A kwanan nan, cibiyar nazarin harkokin kudi ta Chongyang dake jami’ar Renmin ta kasar Sin, ta bullo da rahoton dake cewa, tun daga shekarar 2014 zuwa 1 ga watan Afrilun bana, wato a cikin shekaru 8 ke nan, Amurka da sauran wasu kasashe, sun sanya takunkumai 8,068 ga kasar Rasha, abun da ya sa Rashan zarce Iran wajen zama kasar da ta fi fuskantar takunkumi a duk duniya. Kaza lika tun daga ranar 22 ga watan Fabrairun bana, yawan sabbin takunkuman da aka sanyawa Rasha sun kai 5,314. (Murtala Zhang)