Cibiyar tattalin arzikin Nigeria ta shirya kafa cibiyar kula da cutar tsiron mahaifa ta Endometriosis
2022-03-25 10:35:18 CMG Hausa
Hukumomi a jihar Lagos, cibiyar tattalin arzikin Nijeriya, na shirin kafa cibiyar kula da cutar tsiron wajen mahaifa ta Endometriosis.
Kwamishinan lafiya na jihar Akin Abayomi ne ya bayyana haka a jiya, inda ya ce cibiyar za ta inganta wayar da kai da tunkarar cutar, wadda tsiron da ya kamata ya kasance cikin mahaifa, ke tsirowa a waje, lamarin dake haifar da ciwo da zubar jini.
A cewarsa, cutar, wadda ke shafar kimanin kaso 20 cikin dari na matan Nijeriya, na haifar da matsanancin ciwon mara da ciwo yayin al’ada. Yana mai cewa, tana iya haifar da matsalar haihuwa a tsakanin kaso 40 na matan dake fama da ita.
Ya ce babban kalubalen da ake fuskanta dangane da cutar shi ne, ganowa da kuma maganinta. (Fa’iza Mustapha)