logo

HAUSA

Babban jami’in tsaro: Iran zata ci gaba da halartar tattaunawar Vienna har sai an cimma yarjejeniya mai karfi

2022-03-15 10:38:25 CRI

Babban jami’in tsaron kasar Iran ya sanar a ranar Litinin cewa, kasar Iran zata ci gaba da halartar tattaunawar Vienna da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliyar kasar ta 2015 har sai an kai ga cimma yarjejeniya mai karfi, tare da biya mata muradunta na shara’a da sauran muhimman bukatun kasar.

A sakon da ya wallafa a shafin twita, sakataren majalisar tsaron kasar Iran, Ali Shamkhani, yace dukkan kokarin da Iran take yi tafi mayar da hankali ne wajen kiyayewa da kuma daga matsayin moriyar kasar duk da irin matsayin matsin lambar da kasar ke fuskanta a ciki da wajen kasar. (Ahmad)