logo

HAUSA

Idan har Sin da Amurka suka bude kofa ga juna, bai kamata su sake rufe ta ba.

2022-03-11 13:54:29 CRI

 

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana Jumma’ar nan cewa, yau shekaru 50 da suka gabata, kasashe Sin da Amurka sun karya shingen dake kawo tarkani ga alakar dake tsakaninsu, tare da fara kokarin daidaita dangantakar dake tsakaninsu. Ganin yadda bangarorin biyu suka bude kofa ga juna, to bai kamata a sake rufe ta ba, balle ma a raba ta.

Li Keqiang ya kara da cewa, ko da an samu takara a fannin kasuwa tsakanin Sin da Amurka a fannonin tattalin arziki da cinikayya, kamata ya yi ta kasance mai tsafta da adalci. A bara, yawan darajar cinikayyar da ke tsakanin kasashen biyu, ta zarce dalar Amurka biliyan 750, wanda ya karu da kusan kashi 30 cikin dari bisa na shekarar 2020. Hakan a cewarsa ya nuna cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka na da babban tasiri. Idan Amurka ta sassauta takunkuman hana fitar da kayayyaki da ta sanya kan kasar Sin, adadin cinikin dake tsakanin kasashen biyu zai fi haka, wanda kuma zai amfanawa kasashen biyu da kuma jama'arsu. (Ibrahim)