Dangane da lamarin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yau Jumma'a 12 ga wata cewa, kasar Sin tana maraba da kulla wannan yarjejeniyar, kuma ta nuna yabo ga bangarorin biyu dangane da kokarinsu na shimfida zaman lafiya a kasar da kuma neman sulhunta jama'ar kasar. A matsayinta aminiyar kasar Mozambique, kasar Sin tana fatan bangarorin da abin ya shafa na kasar Mozambique za su ci gaba da dukufa don samun dauwamammen zaman lafiya da bunkasuwar kasar. (Maryam)