in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mafarauta za su fuskanci hukunci mai tsanani a kasar Mozambique
2014-04-11 10:31:14 cri
Mafarauta da ma sauran masu fataucin namun daji za su fuskanci hukunci mai tsanani a kasar Mozambique, da zai kaiwa ga zaman yari shekaru 8 zuwa 12 da kuma tarar dalar Amurka kusan dubu 90, bayan da 'yan majalisar dokokin kasar suka aminci bisa yawan rinjaye a karatun farko da dokar da ta shafi kare kebabbun wuraren namun daji na kasar.

Wannan shirin doka zai yanke zaman yari na shakaru 8 zuwa 12 ga dukkan mutanen da za su kashe namun daji ba tare da izini ba, musammun ma namun dajin dake ake karewa daga bace a doron duniya, ko kuma mutanen da za su yi amfani da wasu hanyoyin da aka haramta na kamun kifi, kamar amfani da nikiya ko wata guba.

Haka kuma mutanen da aka tabbatar da laifin gudanar da ayyukan da aka haramta na ajiya, jigila ko sayar da namun dajin da ake kiyayewa za'a ci tararsu da ta kai dalar Amurka 4425 zuwa 88500. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China