Bangaren 'yan sandan ya bayyanawa 'yan jarida cewa, bisa kididdigar da aka yi, an ce, jam'iyyar RENAMO ta kai hare-hare sau 29 a watan Yuni, yawancinsu an kai su ne a kan motoci dake kan hanyoyin dake a tsakanin arewaci da kudancin kasar. Hare-haren da jam'iyyar ta kai sun haddasa mutuwar fararen hula 6, kuma 21 daga cikinsu sun ji rauni mai tsanani. Yawan mutane da suka mutu ko suka ji rauni a watan Yuni a sakamakon hare-haren ya karu sosai bisa na watan Mayu.
Ban da wannan kuma, an ci gaba da yin shawarwari a tsakanin wakilan gwamnatin kasar Mozambique da na jam'iyyar RENAMO, amma har yanzu bangarorin biyu ba su cimma daidaito kan tsagaita bude wuta a tsakaninsu da shigar da dakarun jam'iyyar zuwa sojojin kasar ba. (Zainab)