Firaminista Vaquina ya fadi haka ne a yayin da yake ganawa da jakadan Sin a Mozambique, Li Chunhua a fadar firaministan kasar. Yayin da ya waiwayi wasu batutuwan tarihi, Vaquina ya furta cewa, ganin yadda al'ummar kasar Mozambique ta yi fama da mulkin mallaka na zalunci a can baya, shi ya sanya jama'ar kasar sun fahimci matsalolin da jama'ar Sin suka fama da su a lokacin baya.
Dadin dadawa, mista Vaquina ya jaddada cewa, dole ne a rike da tarihi, da mutunta abubuwan tarihi, domin cimma burin wanzar da zaman lafiya a duniya, da sa kaimi ga samun ci gaba tare.(fatima)