A baya dai jam'iyyar ta Renamo ta taba bayyana cewa, za ta kauracewa babban zaben dake tafe, da ma na kananan hukumomin kasar da aka shirya a watan jiya, muddin ba a gudanar da sauye sauye ga dokokin zaben kasar ba.
Yayin da Dhlakama ke zantawa da kafofin yada labarun kasar Portugal, ya jaddada cewa, yanzu haka gwamnatin na bukatar yin gyare-gyare a fannin siyasa, ciki hadda batun sabuwar dokar zabe, da yin gyare-gyare ga tsarin dokokin da ke kawo cikas ga tsarin demokuradiyya, a sa'i daya kuma ya nuna damuwa ga rashin cimma matsaya guda, game da shawarwarin da ake yi tsakanin gwamnati da jam'iyyar ta Renamo.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, a karkashin inuwar jam'iyyar Renamo, Dhlakama zai shiga babban zaben da za a yi a ranar 15 ga watan Oktobar badi. Kuma bisa dokokin kasar Mozambique, shugaban kasar mai ci Armando Emílio Guebuza ba shi da ikon sake tsayawa takara, matakin da zai sanya babban zaben kasancewa wata dama ta fidda shugaban kasar na 4, tun bayan kafuwar Mozambique a shekarar 1975.(Bako)