An sake yin musayar wuta tsakanin sojojin gwamanti da dakarun jam'iyyar adawa a Mozambique
Jiya Alhamis 15 ga wata, sojojin kasar Mozambique da dakarun babbar kungiyar adawa ta Mozambican National Resistance sun yi musayar wuta a lardin Zambezia dake yankin tsakiyar kasar, inda aka halaka sojojin gwamnati guda biyu, yayin guda daya ya jikkata. Wannan musayar wuta ita ce ta farko bayan mako daya da kungiyar adawa ta sanar dakatar da kai hare-hare kan sojojin gwamnati da jama'ar kasar.
Ya zuwa yanzu, ba a samu labarin adadin dakarun da suka mutu daga bangaren mayakan ba a yayin musayar wutar, kana bisa labarin da aka samu, an ce, sojojin gwmnatin sun kama dakakru biyu a yayin wannan musayar wuta.(Maryam)