Wani jami'in sashen zirga-zirgar sararin samaniya na kasar Mozambique ya fayyace a ran 21 ga wata cewa, bisa kwarya-kwaryar binciken da aka yi, ya zuwa yanzu an gano dalilin faduwar jirgin fasinja na kasar da ya faru a ranar 29 ga watan jiya, inda aka tuhumi matukin jirgin da sakaci.
Da misalin karfe 9 da minti 26 na safiyar ranar 29 ga watan Nuwamba bisa agogon Greenwich, wannan jirgji na kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Mozambique ya tashi daga Maputo, a kan hanyarsa ta zuwan birnin Luanda, babban birnin kasar Angola. Amma bayan awoyi biyu da tashinsa, an rasa yin tumtubarsa da hedkwata kamfanin a yankin da ke arewacin kasar Namibiya. Bayan haka, 'yan sandan Namibiya suka samu labarin faduwar jirgin. Wannan hadari dai ya yi sanadiyyar rasuwar ma'aikata 6 da ke aiki a cikin jirgin, da sauran fasinjoji 27 ciki har da wani Basinne.
A ran 21 ga wata, shugaban Jami'ar koyar da fasahohin tukin jirgin sama ta kasar Mozambique Mista Joao Abreu ya bayyana a gun wani taron manema labaru cewa, bisa nazarin da aka yi kan bayanan da aka samu daga akwatin da ke dauke da bayani wato black box, da kuma wasu rahotannin da abin ya shafa, an ce, an tabbatar da cewa matuki ne ya haddasa faduwar jirgin da gangan. Mista Abreu ya yi nuni cewa, kafin faduwar jirgin, matukin ya sarrafa jirgin a jere ta yadda zai fado.(Danladi)