Rahotanni daga kasar Mozambique na cewa, mai yiwuwa ne a kai ga cimma matsayar kawo karshen rashin jituwa tsakanin tsagin gwamnati da na 'yan tawayen Renamo nan da ranar Laraba.
Hakan a cewar jagoran kungiyar 'yan tawayen ta Renamo Saimone Macuiana, ya biyo bayan tattaunawar da sassan biyu ke ci gaba da gudanarwa ne a yanzu haka.
Macuiana wanda ya shaida wa manema labaru wannan ci gaba, gabanin halartarsa taron tattaunawar da sassan suka gudanar a jiya Litinin, ya kara da cewa, kungiyarsa na da burin tantance hakikanin yadda za a aiwatar da yarjejeniyar da za a cimma, domin kaucewa matsalolin daka iya biyo baya.
Shi ma a nasa bangare, jagoran tawagar gwamnatin kasar yayin tattaunawar da ke gudana, kuma ministan sufurin kasar Gabriel Muthisse, cewa ya yi, sassan biyu sun sha alwashin cimma matsaya guda, game da dukkanin batutuwan da suka jibanci wannan yarjejeniya dake daf da kammalawa.
An dai kusa kaiwa ga rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhun a zama na 67, da sassan biyu suka gudanar a ranar Larabar da ta gabata, kafin daga bisani kungiyar Renamon ta gabatar da sabuwar bukatar tantance wasu batutuwa da suka jibanci yarjejeniyar.(Saminu Alhassan)