in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Mozambique ya yaba ma kasar Sin bisa taimakonta wajen gina kasar
2014-01-17 15:31:23 cri

Shugaban kasar Mozambique Armando Guebuza ya gode ma kasar Sin bisa ga taimakon ta wajen gina kasar.

Shugaban ya yi jawabin ne a wani bikin da aka shirya domin aza harsashi ga cibiyar taron kasa da kasa na Joaqium Chissano a Maputo, babban birnin kasar a ranar alhamis 16 ga wata.

Mista Guebuza ya bayyana cewa, dangantaka a tsakanin Mozambique da Sin ta kullu tun zamanin da Mozambique take neman 'yancin kanta da tsai da harshen kasa baki daya, daga baya kasashen biyu suna ta kokarin sada zumunci tsakanin su. Ya lura da cewa a waccan zamanin da aka yi fama da karancin ruwan sha da wutar lantarki, da abinci, kwararru daga Sin sun je kasar ta Mozambique domin taimaka mata ba tare da kasala ba, kuma sun samar da fasahohi ga jama'ar kasar da a lokacin suke cikin mawuyacin hali. Ya kara da cewa, har zuwa yau, kwararru Sinawa suna kokari tare da jama'ar Mozambique, domin shiga cikin aikin sake gina kasar Mozambique da raya tattalin arzikin ta, don kafa wata kyakkyawar kasa ga jama'ar Mozambique.

A nasa jawabin Jakadan kasar Sin da ke kasar Mozambique Mista Li Chunhua ya yi bayanin cewa, a 'yan shekarun baya, gwamnatocin kasashen biyu sun kara zurfafa hadin kansu, da raya dangantakarsu, da kuma habaka hadin kansu a fannoni daban daban.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China