Sanarwar ta ce, ana ci gaba da rikici tsakanin sojojin gwamnatin kasar, da ke karkashin shugabancin jam'iyyar Partido Frelimo, da bangaren adawa mafi girma wato jam'iyyar Renamo, abun da ya kawo mummunan tasiri ga aikin gona a kasar, musamman ma a lardin Sofala wanda ke yankin tsakiyar kasar. Don haka, sanarwar ta yi kira ga bangarorin biyu da su gaggauta kawo karshen fito-na-fito da rikici a tsakaninsu.
An samu hatsin da yawansa ya kai sama da kashi 90 cikin 100 a kasar daga filayen manoma da yawansu ya kai kimanin miliyan 3.2. A kuma cikin shirin raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar, gwamnatin Mozambique ta yi shirin habaka aikin gona da yawansu ya kai kashi 7.1 cikin 100 a nan gaba.(Bako)