Wata sanarwar da firaminista May ta fitar jiya daddadare, ta ce rundunar sojin kasar za su ba da taimako ga aikin tunkarar kalubalen ta'addanci, inda za su gudanar da ayyuka a wasu sassan kasar.
Amma ta yi kira ga al'ummomin kasar su ci gaba da yin ayyuka da zaman rayuwarsu kamar yadda suka saba, sannan akwai bukatar su mai da hankali kan harkokin da suka shafi tsaro tare da hada hannu da 'yan sandan kasar.
Da safiyar jiya Jumma'a ne wasu abubuwa suka fashe, a wata tashar jirgin karkashin kasa dake yammacin birnin London na kasar Burtaniya, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane a kalla 29.
'Yan sandan yankin sun sanar da cewa, sakamakon kwarya-kwaryar bincikensu ya shaida cewa, 'yan ta'adda ne suka kitsa harin. (Maryam)