in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Canada ya yi Allah wadai da hari a London
2017-03-23 11:15:38 cri
Jiya Laraba, firaministan kasar Canada Justin Trudeau ya fidda wata sanarwa a birnin Ottawa, inda ya yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kaddamar a birnin London na kasar Burtaniya, kana ya jaddada cewa, kasar Canada tana tare da Burtaniya wajen yaki da ta'addanci.

Sa'an nan, a madadin al'ummomin kasar Canada, Mr. Trudeau ya bayyana cewa, suna goyon bayan firaministar Burtaniya da al'ummomin kasar, kuma a ko da yaushe Canada tana son ba da taimako ga Burtaniya, wajen zakulowa tare kuma da gurfanar da wadanda suka aikata wannan laifi a gaban kuliya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China