Firaiministan Burtaniya za ta jagoranci taron gaggawa sakamakon harin ta'addanci a arewacin London
Firaiministar Burtaniya Theresa May ta fada a yau Litinin cewa za ta halarci taron ganawa ta gaggawa bayan da 'yan sanda suka bayyana lamarin da ya faru a arewacin London da cewa yana da nasaba da harin ta'addanci.
Da safiyar ranar Litinin ne wata motar bas ta bi ta kan wasu al'ummar musulmi da suka taru domin yin ibada a wani masallaci dake arewacin London, inda mutum guda ya rasu, kana wasu mutanen 10 suka jikkata. (Ahmad Fagam)