in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gamayyar kasa da kasa sun yi Allah wadai da harin da aka kai a Manchester
2017-05-24 10:30:19 cri
Bayan aukuwar harin bam din da aka kai a birnin Manchester na kasar Ingila a ran 22 ga wata, babban magatakardan MDD da wasu shugabannin kasashen da suka hada da na Amurka da Rasha da sauransu sun yi Allah wadai da harin, inda suka kuma yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su hada kansu domin yaki da ta'addanci.

A jiya Talata ne, babban magatakadan MDD ya fidda wata sanarwa ta hannun kakakinsa, inda ya yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai a birnin na Manchester, yana mai fatan za a gurfanar da wanda ya aikata laifin a gaban kuliya.

A jiya ne kuma, yayin zantawarsa da firaministar kasar Ingila Theresa Mary May ta wayar tarho, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi Allah wadai da harin da ya auku a kasar Ingila. Sa'an nan, fadar White House ta kasar Amurka ta fidda wata sanarwa, inda a ciki shugaba Donald Trump ya jaddada cewa, a shirye kasar Amurka ta ke ta baiwa Ingila dukkan taimakon da ya dace domin gudanar da bincike kan harin.

Shi ma shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya aike da sakon alhini ga Theresa May, inda ya bayyana cewa, kasar Rasha tana shirya inganta hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Ingila kan ayyukan yaki da ta'addanci bisa shirye-shiryen da aka kulla a tsakanin kasashen biyu da kuma a tsakanin kasa da kasa.

Ban da haka kuma, wasu shugabannin kasashe da suka hada da na Jamus, Faransa da kuma Isra'ila da sauransu sun fidda sanarwa domin yin Allah wadai da harin da ya auku a kasar Ingila.

Rundunar 'yan sandan birnin Manchester ta sanar da cewa, mutane 22 ne suka mutu, kana wasu 59 kuma suka jikkata sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a daren ranar 22 ga wata a filin wasa na Manchester dake Ingila. Daga bisani kuma kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai harin ta shafinta na yanar gizo. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China