Firaministar Burtaniya Madam Theresa May ta sanar da daukar tsauraran matakan yaki da ayyukan ta'addanci a kasar, ciki har canja dokokin da suka shafi kare hakkin bil-Adama da ake amfani da su a kasar.
Madam May ta zayyana wadannan matakai da take son gabatarwa ne yayin gangamin yakin neman zabe a Slough gabanin ranar karshe ta yakin neman zaben na babban zaben kasar.
Sai dai yayin da kasar ke jimamin hare-haren da aka kai a biranen Landan da Mancherster, da al'amun firaministar ta himmatu wajen nunawa masu kada kuri'a cewa, idan har ta lashe babban zaben, hakika za ta magance barazanar ta'addanci da kasar take fuskanta.(Ibrahim)