Da safiyar yau Jumma'a ne wasu ababen fashewa suka tashi, a wata tashar jirgin karkashin kasa dake yammacin birnin London na kasar Ingila, lamarin da ya sabbaba jikkatar wasu mutane. 'Yan sandan wurin sun sanar da cewa, kwarya-kwaryar sakamakon bincikensu ya shaida cewa, 'yan ta'adda ne suka kitsa lamarin.
A dai yau din, kakakin firaministar Ingila ya cewa, madam Theresa May ta maida hankali matuka game da aukuwar harin, tana kuma tuntubar sassa masu ruwa da tsaki, domin kara fahimtar abun da ya faru a kan lokaci. (Tasallah Yuan)