in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sin ya mika sakon alhini ga sarauniyar Burtaniya
2017-03-23 14:06:08 cri
Yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon nuna alhini ga sarauniyar kasar Burtaniya Elizabeth II, don gane da harin ta'addanci da aka kaddamar a birnin London, inda ya kuma yi Allah wadai da harin, yana mai bayyana juyayi game da rasa rayuka da aka yi a harin.

Bugu da kari, ya ce, kasar Sin na adawa a dukkan wani nau'i na ta'addanci, tana kuma fatan karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasar Burtaniya, har ma da gamayyar kasa da kasa, a fannin kiyaye tsaron kasashen duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China