in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi faretin soja don murnar ranar haihuwar sarauniyar Ingila
2016-06-12 13:21:17 cri

An gudanar da kasaitaccen faretin soja, a cibiyar birnin London a jiya Asabar, a wani bangare na bikin murnar kewayowar ranar haihuwar sarauniyar Ingila Elizabeth II, wadda a bana ta cika shekaru 90 a duniya.

Sojoji fiye da 1600 da dawaki fiye da 300 ne suka halarci faretin. Wannan dai biki shi ne mafi kasaita da aka shirya a birnin na London, tun bayan bikin auren yarima William Philip da aka gudanar a shekarar 2011.

Ranar 21 ga watan Afrilu ce dai hakikanin ranar haihuwar sarauniya Elizabeth II, amma bisa al'adar gargajiyar gidan sarautar kasar Birtaniya, ana gudanar da bikin murnar ranar haihuwar sarki ko sarauniya ne a ranar Asabar ta tsakiyar watan Yuni. Za kuma a kwashe kwanaki 3 ana shagalin bikin na wannan karo.

Sarauniya Elizabeth II, ta hau gadon sarauta ne a ranar 6 ga watan Febarairun shekarar 1952, ta kuma kwashe shekaru 64 a karagar mulki, inda ta zama sarauniya mafi dadewa a wannan karaga a tarihin kasar.

Kaza lika dan ta yarima Charles, shi ne yarima mai jiran gadon sarauta da ya fi kowane yarima dadewa a wannan matsayi, domin a yanzu haka ya kai shekaru 67 da haihuwa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China