A jiya Laraba ne, rundunar 'yan sandan kasar Burtaniya ta tabbatar da cewa, gobarar da ta tashi a wani dogon bene dake yammacin birnin London na kasar Burtaniya a safiyar wannan rana, ta haddasa rasuwar mutane guda 12, kuma a halin yanzu, akwai mutane 68 da ke samun kulawa a asibiti.
'Yan sandan birnin London sun bayyana cewa, ana gudanar da bincike kan dalilin tashin gobarar, kuma mai iyuwa ne, a yayin da suke ci gaba da aikin ceto, adadin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata na iya karuwa. (Maryam)