Kuma a halin yanzu, ana ci gaba da gudanar da bincike a wurin da gobarar ta tashi, kuma adadin wadanda suka mutu na iya ci gaba da karuwa.
A jiya Asabar, masu zanga-zanga da dama sun taru a wurin dake kusa da fadar firaministan kasar dake kan titin Downing lamba ta 10, domin neman firaministar kasar Theresa May ta yi murabus, sabo da zargin da iyalan wadanda suka rasu suka yi wa gwamnatin kasar Burtaniyan cewar, ba ta yi rigakafi da kuma gudanar da ayyukan agaji yadda ya kamata ba.
Kuma wasu suna ganin cewa, hadarin gobarar da ta tashi a kasar, ya nuna matsalolin kasar Burtaniya kan gudanar da bincike kan yanayin tsaron kasa. Baki daya akwai irin wannan dogon bene kimanin dubu hudu a duk fadin kasar Burtaniya, kuma galibi an gina su ne daga shekarar 1950 zuwa shekarar 1970 na karnin da ya gabata.
A safiyar ranar 14 ga wata ne, gobara ta tashi a wani dogon bene mai suna Grenfell Tower, inda mutanen kasar suke zama a ciki. Firaministar kasar Theresa May ta ba da umurnin gudanar da bincike kan wannan hadari. (Maryam)