Mr. Lavlov ya bayyana haka ne, a yayin taron manema labaran na hadin gwiwa tsakaninsa da takwaransa na kasar Qatar Sheikh Sabah Al-Khaled Al-Hamad Al-Sabah.
Ya kuma kara da cewa, ya kamata a warware matsalar bisa tsarin kungiyar hadin gwiwar kasashen yankin Gulf wato GCC.
A nasa bangare, Mr. Al-Sabah ya jaddada cewa, ya kamata a warware matsalar ta hanyar shawarwari tsakanin bangarori daban daban, don tabbatar da tsaron kasar Qatar da kasashen yankin Gulf.
A farkon watan Yuni na bana ne, kasashen hudu suka katse huldar diflomasiya tsakaninsu da kasar Qatar bisa zargin cewa, kasar Qatar tana goyon bayan 'yan ta'adda, lamarin da ke haifar da barazana ga yanayin tsaron yankin, zargin da Qatar din ta musanta, haka kuma, kasashen hudu suka fara hana jigilar kayayyaki a tsakaninsu da kasar Qatar. Daga bisani kuma, wasu kasashe suka sanar da katse huldar jakadanci da kasar ta Qatar.
Amma har yanzu, ba a kai ga sassauta wannan matsala ba. (Maryam)