in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu dalilin yanke huldar diplomasiyya da Qatar, in ji mahukuntan kasar
2017-06-05 19:01:19 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Qatar, ta fitar da sanarwa a yau Litinin, inda ta nuna mamaki da takaici, game da yanke huldar diplomasiyya da wasu kasashen suka yi da ita. Kasashen da suka yanke hulda da kasar dai sun hada da Saudiya, da hadaddiyar daular Larabawa, da Bahrain, amma ba a ambaci kasar Masar kai tsaye ba.

A cewar sanarwar, kasar Qatar mambar GCC ce, kuma tana bin tsarin mulkin kan ta, da girmama sauran kasashe, kana ba ta taba tsoma baki kan harkokin gida na wasu kasashe ba. A hannu guda muma tana daukar nauyin yaki da ta'addanci da yunkurin dakile masu tsattsauran ra'ayi. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China