in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dole Qatar ta cimma sharuddan bukatu 13 da aka gabatar mata, in ji wasu kasashen Larabawa
2017-07-31 10:52:32 cri
A jiya Lahadi ne, wasu kasashen Larabawa hudu, wadanda suka hada da Saudiyya, da Masar, da Hadaddiyar Daular Larabawa, gami da Bahrain, sun fitar da wata sanarwa, inda suka jaddada cewa, za su yi shawarwari tare da kasar Qatar ne kawai, idan ta cimma manyan sharuddan goma sha uku da suka gabatar mata.

A jiyan ne, ministocin harkokin kasashen wajen kasashen Saudiyya, da Masar, da Hadaddiyar Daular Larabawa, gami da Bahrain suka tattauna a tsakaninsu. Kuma bayan tattaunawar ce, ministan harkokin wajen Bahrain Khalid Bi Ahmed Bin Mohammed Al-Khalifa ya jaddada cewa, kasashen hudu sun bukaci Qatar da ta dakatar da duk wani yunkurinta na goyon-bayan ayyukan ta'addanci, da kuma daukar wasu matakai na garkamawa Qatar takunkumi, al'amuran da suka dace da dokokin kasa da kasa. Har wa yau, kasashen hudu suna nan a kan bakarsu kan wannan matsayi da suka dauka.

A nasa bangare, ministan harkokin wajen Saudiyya Adel al-Jubeir ya karyata zargin da Qatar ta yi mata wai cewar, Saudiyya ta hana musulmanta zuwa aikin hajji, inda ya ce, Saudiyya ba ta yarda Qatar ta saka batun siyasa cikin aikin hajji ba, don haka Saudiyya tana maraba da musulman Qatar dake da niyyar zuwa Makka don aikin hajji. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China