in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Chadi ta garkame ofishin jakadancin Qatar
2017-08-24 09:21:12 cri
Mahukunta a kasar Chadi sun bada umarnin garkame ofishin jakadancin kasar Qatar dake birnin Ndjamena, tare da baiwa ma'aikatan sa wa'adin kwanaki 10 na ficewa daga kasar. Chadi dai na zargin Qatar din da kokarin tada zaune tsaye a kasar ta kafar kasar Libya.

Wata sanarwa da mahukuntan Chadin suka fitar, ta ce daukar wannan mataki ya zama tilas, idan aka yi la'akari da illar da Qatar din ka iya yiwa Chadi idan har ba a gaggauta daukar matakai ba.

Kaza lika sanarwar ta ce nan da 'yan kwanaki, Chadi za ta rufe na ta ofishin jakadancin dake Qatar tare da maida ma'aikatan sa gida, duka dai da nufin wanzar da zaman lafiya da lumana a kasar da ma yankin da ta ke.

A watan Yunin da ya gabata ma dai kasashen Chadi, da Mauritania da Senegal sun bi sahun Saudiya da sauran kasashen larabawa, wajen janye jakadun su daga Qatar.

Hakan kuwa ya biyo bayan daukar makamancin wannan mataki ne da Saudiyya tare da wasu kawayen ta suka yi, inda kasashen suka katse huldar jakadanci da kasar ta Qatar tare kuma da rufe kan iyakokin su na sama, da kasa, da ruwa dake tsakanin su da kasar, tun daga ranar 5 ga watan Yunin da ya gabata.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China