Sanarwar da ma'aikatar ta fitar a wannan rana ta yi nuni da cewa, Qatar ba za ta dauki matakai kan mutanen da ke cikin kasar, wadanda kasashensu suka katse huldar jakadanci da ita ba, haka kuma ba za ta dauki matakai na rage matsayin huldar jakadanci da su ba.
Sanarwar ta jaddada cewa, 'yan kasashen da suka katse huldar jakadanci da kasar Qatar, wadanda suke rayuwa a cikin kasar suna da cikakken 'yanci.
A labarin da aka bayar, an ce, kasashen Saudiyya, da hadaddiyar daular Labarawa, da ma sauran wasu kasashe tuni sun bukaci al'ummarsu da su bar Qatar, haka kuma sun bukaci mutanen kasar Qatar da su fita daga kasashen cikin kwanaki 14 tun bayan da aka katse huldar jakadancin.
Kwanan nan kasashen Bahrain da Saudiyya, da hadaddiyar daular Larabawa, da Masar, da Yemen, sun sanar da katse huldar jakadancin da kasar Qatar, inda suka zargi Qatar da nuna goyon baya ga ayyukan ta'addanci, tare kuma da lalata zaman lafiya a shiyyar.
A game da wannan, ma'aikatar harkokin waje ta Qatar ta bayyana bakin cikinta, tana mai cewa, wannan mataki ko kadan ba shi da dalili. (Lubabatu)