in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Erdogan da sarkin Saudi sun tattauna batun warware rikicin Qatar
2017-07-24 14:05:04 cri
A matsayin wani sabon yunkuri na warware takaddamar dake tsakanin Qatar da kasashen larabawa, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya gana da sarkin Saudiyya Salm bin Abdulazizi a ranar Lahadi, inda suka tattauna game da batun diplomasiyya da nufin warware dakaddamar dake tsakanin kasar Qatar da kasasshen larabawa wanda Saudiyyar ke jagoranta.

Shugabannin biyu sun kuma tattauna game dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da irin cigaban da aka samu a shiyyar, bugu da kari sun jaddada muhimmancin daukar matakan yaki da ta'addanci, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Saudiyyan ya rawaito.

Rangadin da Erdogan yake gudanarwa a yankin Gulf, zai kunshi har da kasashen Qatar da kuma Kuwait, ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da Turkiyyar ke burin kawo karshen tsamin dangantaka dake wanzuwa a tsakanin kasashen na yankin Gulf.

Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu, ya gudanar da makamanciyar wannan ziyarar a watan jiya da nufin tabbatar da maslaha a tsakanin kasashen, sai dai ziyarar bata haifar da wani sakamako mai armashi ba.

Kasashen yankin larabawa wanda Saudiyya ke jagoranta, da suka hada da Hadaddiyar daular laraba UAE, Bahrain, da Masar, sun yanke hulda da kasar Qatar ne tun a ranar 5 ga watan Yuni, bisa zarginta da hannu wajen taimakawa ta'addanci, zargin da Qatar din ta sha musantawa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China