Mr. Jubeir ya ce, kasashen hudu da suka hada da Saudiya, da Masar, da Hadaddiyar daular Larabawa da kuma Bahrain, ba za su yi shawarwari da kasar Qatar kan bukatun da suka gabatar mata ba.
Haka kuma, bisa labarin da aka samu, an ce, ministan harkokin wajen kasar Qatar Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani zai kai ziyarar aiki a kasar Amurka, domin tattaunawa da bangaren Amurka, kan matsalar katse huldar jakadanci da kasar sa ke fama da ita a halin yanzu.
A ranar 5 ga watan nan ne, kasashen hudu suka katse huldar jakadanci dake tsakaninsu da kasar Qatar bisa zargin cewa, kasar Qatar tana goyon bayan 'yan ta'adda, wadanda ke haifar da barazana ga yanayin tsaron yankin, sa'an nan, kasashen hudu sun fara hana jigilar kayayyaki a tsakaninsu da kasar Qatar.
Daga bisani kuma, wasu kasashe sun sanar da katse huldar jakadanci dake tsakaninsu da kasar Qatar.
Bisa labarin da aka fidda a ranar 23 ga wata, an ce, kasashe hudu sun riga sun gabatar da bukatu guda 13 ga kasar Qatar, domin warware matsalar katse huldar jakadancin da ita, inda suka kuma bukaci kasar Qatar da ta amince da bukatunsu cikin kwanaki 10. To sai dai kuma Qatar din ta bayyana cewa, bukatun da kasashen hudu suka gabatar mata, sun sabawa 'yancin mulkin kasar. (Maryam)