Sakataren wajen kasar Amurka Rex Tillerson, ya koma gida daga kasar Saudiyya, bayan da ya tattauna da ministocin harkokin wajen kasashen nan 4, wadanda suka katse dangantaka da Qatar. Sai dai kuma rahotanni sun bayyana cewa Mr. Tillerson bai bayyana wata matsaya game da ganawar ta su ba.
Ganawar jami'an dai ta zo ne bayan da Mr. Tillerson din ya kammala ziyara a Kuwait da Qatar, ya kuma rattaba hannu kan wata yarjejeniya da mahukuntan Qatar, game da hanyoyin dakile samarwa 'yan ta'adda kudade.
A daya hannun, bayan wannan yarjejeniya ta Qatar da tsagin Amurka, kasashen 4 sun fidda wata sanarwar hadin gwiwa a ranar Talata, wadda ke cewa sai da aka kai ruwa rana, kafin a cimma matsaya tsakanin Amurka da kasar ta Qatar game da daukar matakan dakile yaki da ta'addanci tare da kasar ta Qatar.(Saminu Alhassan)