in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Erdogan: sharudan da aka shata ma Qatar sun saba wa doka
2017-06-26 09:09:15 cri
Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya ce sharudan da aka shata ma kasar Qatar don daidaita matsalar dakatar da hulda da ita sun saba wa dokokin kasa da kasa.

Shugaba Erdogon ya yi furucin ne a ranar Lahadi da ta gabata, inda ya gaya ma kafofin watsa labaru cewa wasu sharuda guda 13 da aka shata ma kasar Qatar ba daidai ba ne. Dangane da yadda aka bukaci Qatar da ta dakatar da gina wasu sansanonin sojojin kasar Turkiya a kasar, shugaba Erdogan ya ce, hadin gwiwar da ake yi tsakanin kasar Turkiya da sauran kasashe a fannin aikin soja ba ta bukatar samun izini daga sauran kasashe.

Tun daga ranar 5 ga watan da muke ciki, kasashen da suka hada da Saudi Arabiya, hadaddiyar daular Larabawa ta UAE, Bahrain, da Masar sun sanar da yanke huldar dake tsakaninsu da kasar Qatar, bisa dalilin cewa Qatar tana goyon bayan ta'addanci, da yunkurin ta da zaune tsaye a yankin da kasashen suke ciki.

Bayan haka kuma kasashen sun gabatar da wasu sharuda guda 13 ga Qatar, don daidaita matsalar yanke huldar dake tsakaninsu. Sharudan da suka hada da janye jami'an diplomasiya na kasar Qatar daga Iran, da dakatar da hadin gwiwar aikin soja tsakanin Qatar da Iran, da rufe gidan telabijin din al-Jazeera, da dakatar da gina sasannin soja na kasar Turkiya a Qatar, da dai sauransu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China