in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya ya gana da ministan wajen kasar Sin
2017-01-12 09:39:56 cri

Jiya Laraba 11 ga wata, shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a babban birnin kasar, Abuja.

A yayin ganawar tasu, shugaba Buhari ya mika gaisuwarsa ga shugaba Xi Jinping, inda ya bayyana cewa, a lokacin da ya kai ziyarar aiki a kasar Sin a shekarar da ta gabata, ya cimma matsaya daya da shugaba Xi Jinping kan zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, sa'an nan, Nijeriya ta dauki matakai da dama domin aiwatar da harkokin da suka cimma ra'ayi daya yadda ya kamata. Bugu da kari, kasar Nijeriya ta kuma cimma alkawarinta na tsayawa tsayin daka wajen kiyaye manufar kasar Sin daya tak, inda ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka ba da sanarwa ta hadin gwiwa a yau.

A nasa bangare, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya mika gaisuwar shugaba Xi Jinping ga shugaba Muhammadu Buhari, inda ya kuma nuna yabo ga kasar Nijeriya dangane da goyon bayan da take baiwa kasar Sin kan kiyaye manufar kasar Sin daya tak, haka kuma, ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da hadin gwiwar dake tsakaninta da Nijeriya wajen aiwatar da sakamakon dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, kana da karfafa hadin gwiwar kasashen biyu kan ayyukan noma, gina layin dogo, hakar ma'adinai da dai sauransu, ta yadda Nijeriya za ta kyautata kwarewarta wajen neman bunkasuwa da kanta. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China