Wang ya ce, dangantakar dake tsakanin Sin da Jamhuriyar Kongo, abar koyi ce ga kasashen dake tasowa a duniya.
Kasar Sin ta bada taimako gami da shiga cikin manyan ayyukan masana'antu da bunkasa tattalin arziki ta hanyoyi daban-daban a kasar ta Kongo.
Kazalika, Wang ya bayyana cewa, kasar Sin ta ba Jamhuriyar Kongo shawarwari game da yankin Pointe-Noire, har ya zamanto wani katafaren aiki na hadin-gwiwar masana'antun Sin da Kongon, da kafa wasu manyan cibiyoyi guda hudu, ciki har da cibiyar jigilar kaya, da cibiyar kere-kere da ta zirga-zirgar jiragen sama da sauransu.
A nasa bangaren, Jean Claude Ngakosso ya nuna cewa, kasar Sin babbar aminiyar cinikayya ce ga Jamhuriyar Kongo, kuma Kongon ta amince da irin ra'ayoyin da gwamnatin kasar Sin ke da su wajen karfafa hadin-gwiwa da ita.
Kongo tana fatan Sin za ta kara taimaka mata wajen raya yankin Pointe-Noire, ta yadda zai samar da alfanu ga al'ummar kasar.(Murtala Zhang)