in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kafa cibiyar nazarin al'adun Sin ta Nijeriya a jami'ar Nnamdi Azikiwe
2016-06-29 10:41:23 cri

A jiya Talata 28 ga wata, an yi bikin bude cibiyar nazarin al'adun Sin ta Nijeriya a kwalejin Confucius na jami'ar Nnamdi Azikiwe dake jihar Anambra ta kasar.

Shugaban jami'ar Joseph Ahaneku ya bayyana cewa, jami'ar Nnamdi Azikiwe za ta yi amfani da rawar kwalejin Confucius, da kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da jami'o'in kasar Sin a fannonin raya al'adu, da kuma tsara burin raya kwalejin Confucius da cibiyar nazarin al'adun Sin a nan gaba. Cibiyar nazarin Sin ta Nijeriya da aka bude za ta samar da damar yin nazari ga masana al'adun Sin da kasashen waje, da sa kaimi ga yada al'adun Sin a Nijeriya har ma a dukkan nahiyar Afirka.

Mashawarci mai kula da al'adu na ofishin jakadancin Sin dake Nijeriya Yan Xiangdong wanda ya halarci bikin ya nuna yabo ga malamai daga Sin na kwalejin Confucius na jami'ar Nnamdi Azikiwe domin sun yi kokarin koyar da Sinanci a Nijeriya da yada al'adun Sin. Malamin ya bayyana cewa, ziyarar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Sin ta zurfafa zumunta a tsakanin kasashen biyu, kafuwar cibiyar nazarin al'adun Sin za ta taka rawar musamman wajen kara yin mu'amala a tsakanin jama'ar kasashen biyu da kuma sada zumunta a tsakaninsu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China