in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Jamhuriyar Kongo ya gana da minsitan harkokin wajen Sin
2017-01-11 09:56:34 cri
Jiya Talata 10 ga watan nan ne, shugaban Jamhuriyar Kongo Denis Sassou-Nguesso, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, a fadarsa dake birnin Brazzaville.

A wajen ganawar, Sassou ya ce, kasashen biyu wato Kongo da Sin, na da daddadiyar dangantaka da ta shafe tsawon shekaru sama da 50, kuma a halin yanzu, tana kara bunkasa kwarai.

Kongo ta yabawa kasar Sin saboda cikakken goyon-bayan da take bata, inda take fatan Sin za ta gudanar da dukkanin ayyukanta a Kongo lami-lafiya.

Bugu da kari, shugaba Sassou ya bayyana cewa, kasarsa na yin tsayin daka wajen marawa kasar Sin baya a wasu muhimman batutuwan da suka shafi cikakken yanki gami da ikon mallakar kasar, ciki har da batun Taiwan da na tekun kudancin kasar Sin.

Sassou ya ce, tabbas kasar Sin za ta samu ci gaba mai dorewa, sannan ta kara taka rawa a harkokin kasa da kasa, karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping.

A nasa bangaren, Mista Wang Yi cewa ya yi, kasashen Sin da Kongo aminan juna ne dake fahimta tare da taimakawa juna. haka kuma, suna zurfafa ayyukan cude-ni-in-cude-ka tsakaninsu.

Kasar Sin ta yi imanin cewa, bunkasar Jamhuriyar Kongo gami da hadin-gwiwarta da Sin na da makoma mai haske.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China