in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta jaddada matsayin ta na amincewa da kasar Sin daya tak a duniya
2017-01-12 09:21:08 cri

Gwamnatin Najeriya ta sake nanata matsayar ta game da aminewa da manufar kasar Sin daya tak a duniya. Ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama ne ya nanata hakan, yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da ya gudanar tare da takwaransa na kasar Sin Wang Yi wanda ke ziyarar aiki a Najeriya.

Ministan ya kara da cewa, Najeriya za ta ci gaba da martaba dadaddiyar alakar dake tsakanin ta da kasar Sin, da ma hadin gwiwa mai alfanu da kasashen ke samu daga juna.

Wata sanarwa ta hadin gwiwa da aka fitar bayan kammala taron manema labaran, ta yi karin haske game da matsayin Najeriyar kan wannan batu. Sanarwar ta ce manufar kasar Sin daya tak a duniya jigo ce, cikin manufofin hadin gwiwar sassan biyu, kuma Najeriya na daukar yankin Taiwan a matsayin bangare na kasar Sin.

Kazalika Sin da Najeriya za su ci gaba da martaba matsayin juna na kasashe masu cikakken 'yancin kai, da iko na kare fadin iyakokin su yadda ya kamata.

A nasa bangare Mr. Wang Yi gode wa mahukuntan Najeriyar ya yi, bisa daukar wannan matsayi na martaba wanzuwar kasar Sin daya tak a duniya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China