Mr. Gu ya bayyana cewa, kasar Sin na fatan ci gaba da karfafa fahimtar siyasa da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, don ciyar da dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare gaba. Ya ce, yana da alfahari sosai domin an nada shi a matsayin jakadan kasar Sin a kasar Nijeriya, kuma yana fatan shugaba Jonathan da gwamanatin kasar za su ci gaba da nuna goyon baya domin ingiza dangantakar kasashen biyu.
A nasa tsokacin kuma, shugaba Jonathan ya nuna maraba da zuwa ga sabon jakadan kasar Sin a kasar Nijeriya Gu Xiaojie, tare da bayyana fatan alherinsa ga shugaban kasar Sin Xi Jinping da kuma firaministan kasar Li Keqiang, sa'an nan, a madadin gwamnati da jama'ar kasar Najeriya, shugaba Jonathan ya nuna juyayi ga iyalan fasinjojin wadanda suka dauki jirgin saman Malaysian da ya bace. Bugu da kari, Mr. Jonathan ya nuna yabo sosai kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Ya ce, a matsayin manyan kasashe masu tasowa, kasar Sin da kasar Nijeriya na da kyakkyawar makoma wajen yin hadin gwiwa, kuma yana fatan jakada Gu zai iya ba da babbar gudumawa wajen ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba cikin wa'adinsa na aiki. (Maryam)