A daren ranar 28 ga watan Nuwamban shekarar 2016 ne, wani da ba a sa kowane ne ba, ya kai hari kan wani dan kasar Sin dake a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa wurin zamansa daga mahakar ma'adinai dake jihar ta Nasarawa.
A lokacin da aka kai harin, Dan asalin kasar Sin din na cikin mota tare da wani Basine dan uwansa da wasu 'yan Nijeriya uku ciki har da dan sanda.
Harin dai, ya yi sanadiyyar rasuwar dan kasar Sin guda daya tare da 'yan Nijeriyar uku, yayin da daya Basinen ya ji rauni. (Maryam)