Mista Onu ya yi wannan furuci ne a wajen taron jam'iyyar APC mai mulkin kasar, inda ya ce, tattalin arzikin Najeriya ya dade yana dogaro kacokan kan fitar da gurbataccen man fetur zuwa kasashen waje, kuma hakan ba zai yi tasiri kan farashin man fetur na duniya ba.
Najeriya kasa ce da Allah ya hore mata dimbin albarkatun man fetur, amma ba ta da karfi sosai wajen tace mai, lamarin da ya sa take shigar da tataccen mai daga kasashen waje.
Kuma wannan, shi ne babban dalilin da ya sa take fuskantar matsalar karancin mai a duk fadin kasar a wasu lokuta.
Game da bayanin da Onu ya yi, wasu masharhanta sun ce, a halin yanzu Najeriya na fuskantar karancin ingantattun kayayyakin tace mai gami da isasshen kudi, shi ya sa suke ganin da kyar ta iya cimma wannan burin na haramta shigar da tataccen man fetur daga kasashen waje a badi.(Murtala Zhang)