Jiragen saman fasinjan na kasashen ketare suna duba yiwuwar dakatar da zirga-zirga a Najeriya biyo bayan matakin da gwamnatin Najeriyar ta dauka na rufe filin jiragen sama na kasa da kasa na Nmandi Azikwe da ke Abuja na wasu 'yan makonni.
Gwamnatin Najeriyar dai ta bayyana cewa, za ta rufe filin jiragen saman na Abuja ne, saboda wasu 'yan gyare-gyaren da za ta gudanar a hanyar tashi da saukar jiragen saman.
Wasu daga cikin manyan kamfanonin jiragen sama na Turai da Amurka sun yanke shawarar dakatar da zirga-zirga zuwa kasar ce saboda matakin gwamnati Najeriyar na mayar da harkokin jiragen saman zuwa filin jiragen sama da ke Kaduna, matakin da kamfanonin jiragen saman suka ce yana da hadari ga 'yan kasashen waje.(Ibrahim)