Waikilai sama da 150 wadanda suka zo daga kwamitin raya tattalin arzikin Afirka na MDD, kungiyar tarayyar kasashen Afirka, gwamnatocin kasashen Afirka da kuma kamfanonin intanet na nahiyar sun halarci wannan taro, inda suka tattauna kan yadda za a raya tattalin arziki na nahiyar baki daya da kuma kyautata zaman rayuwar al'ummomin nahiyar ta hanyar yin amfani da fasahohin intanet.
Ministan harkokin sadarwa da gidan waya na kasar Afirka ta Kudu Siyabonga Cwele ya bayyana cewa, a halin yanzu, intanet ya kasance muhimmin abu ga kasa da kasa wajen neman bunkasuwa, shi ya sa, ya kamata nahiyar Afirka ta gina harkokin intanet da ba da horaswa kan harkokin da abin ya shafa yadda ya kamata, sai dai za ta iya shiga hanyar raya tattalin arziki ta intanet, ta yadda za ta iya fuskantar da kawo kwaskwarima kan masana'antu karo na hudu a duniya yadda ya kamata.
A 'yan shekarun nan, kamfanonin kasar Sin sun ba da muhimmin taimako ga kasashen Afirka wajen raya harkokin intanet, musamman ma kamfanin Huawei, wanda ya kafa cibiyar gwaje-gwaje ta fasahohin sadarwa ta farko a nahiyar Afirka a birnin Johnnesburg na kasar Afirka ta Kudu a watan Yuli na shekarar bana, sa'an nan, cibiyar ta kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da wasu jami'o'I da dama, cikin har da jami'ar Johannesburg, inda zai ba da horaswa ga dalibai da dama kan harkokin da abin ya shafa, ta yadda za a kyautata yanayin kimiyya da fasahar kasar Afirka ta Kudu. (Maryam)