Mutanen kasar Rwanda dake neman bayanai kamar takardun aure da na mutuwa za su iyar samun wadannan bayanai ta hanyar intanet bayan wani sabon shiri na gwamnatin kasar.
Kigali da Ngali Holdings, wani kamfanin kasar Rwanda sun cimma wata yarjejeniya a kwanan baya domin kafa layin internet na Rwanda, wani shirin da zai taimaka wajen samun ayyukan gwamnati ta hanyar intanet, da ma ta wasu mahajojin salula.
Makasudin wannan tsari shi ne cike gibin dake akwai wajen samun bayanai ta intanet ga mutane da kamfanoni, da kuma kyautata ayyuka na jama'a ta hanyar shigar da su cikin fasahar zamani, in ji kwamitin cigaban kasar Rwanda a cikin wata sanarwa.
Fiye da ayyuka dari ne da mutanen kasar suka fi yawan tambaya za su tura yanar gizo, har ma da bayanan aure, aifuwa, mutuwa da lasin mota.
Jean Philbert Nsengimana, ministan matasa da harkokin internet na kasar Rwanda, ya bayyana cewa, wannan tsari shi ne hanya guda ta gudanar da ayyuka yadda ya kamata ga ofisoshin minitoci da ma'akatun gwamnatin kasar Rwanda. (Maman Ada)