in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin jiragen saman Afrika ta Kudu ya hana a shiga Samsung Galaxy Notes 7 a cikin jiragensa
2016-10-20 10:32:22 cri
Kamfanin jiragen saman Afrika ta Kudu (SAA) ya sanar a ranar Laraba da matakin hana a shigar da salula kirar Samsung Galaxy Notes 7 bisa dalilin wasu haduran da aka samu dake nasaba da matsalar baturi, dake janyo wani karin zafi da wasu hadura da ma fashewa.

Dukkan fasinjojin dake rike da Samsung Galaxy Notes 7 ba za a ba su izinin shiga jiragen kamfanin SAA ba, in ji kamfanin a cikin wata sanarwa.

An dauki wannan mataki bisa dalilai na tsaro bayan sanarwar ba da umurni ta kungiyar sufurin jiragen saman kasa da kasa (AITA), in ji kakakin SAA, Tlali Tlali.

Kamfanin SAA ya bayyana cewa dalilin yawan wasu hadura dake shafar fashewar baturi ko wasu haduran da aka samu kan wasu wayoyin Samsung Galaxy Notes 7, tabbas barin a shigar da wannan salula cikin jiragen sama na kasancewa babbar barazana ga fasinjoji da jiragen sama.

Yawancin kamfanonin jiragen saman duniya sun hana a shigar da Samsung Galaxy Notes 7 cikin jiragensu tun watan Satumbar da ta gabata, bayan an gano wasu fashewa da haduran batura kusan goma. Lamarin da ya tilastawa kamfanin Samsung maido da dukkan wadannan wayoyin kasuwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China